News
Ƴan fashin daji na ta kwararowa jiha ta, Gwamnan Nassarawa ya koka
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana damuwa game da yadda gungun ‘yan fashin daji ke tururuwa zuwa jiharsa bayan koro su daga maƙwabtan jihohi.
BBC ta rawaito cewa, Gwamna ya ce jami’an tsaro sun lura da ƙaruwar ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Karu, wadda ke da nisan ƙasa da kilomita 30 daga Abuja babban birnin ƙasar.
An kama mutanen hudu da ake zargin sun taimaka wajen kai hari gidan yarin Kuje
“Mun lura da tarin ‘yan fashin nan da aka koro daga jihohin Kaduna da Katsina da Neja da Kebbi musamman a yankunan Rugan Juli da Rugan Madaki da ke Ƙaramar Hukumar Karu,” a cewar gwamnan yayin taron manema labarai ranar Asabar.
“Kazalika, mun ga wasu daga cikinsu a ƙananan hukumomin Wamba da Toto.”
Haka nan gwamnan ya ce sun yi nasarar kama wasu daga cikin fursunonin da suka tsere daga Gidan Yari na Kuje a Abuja bayan mayaƙan Boko Haram sun fasa shi a watan Yuni.
Wasu mazauna yankunan da Gwamna Sule yake magana sun faɗa wa BBC Hausa cewa sun shaida ƙaruwar satar mutane a yankunan nasu.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
