Connect with us

News

NDLEA ta rufe gidan abinci bisa zargin sayar da kayan maye a Kano

Published

on

Daga yasir sani Abdullahi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ta NDLEA ta rufe wani gidan abinci da take zargin ana sayar da kayan maye tare da kama kusan mutum 51 a Kano.

BBC Hausa ta rawaito cewa hukumar ta NDLEA ta ce ta kama mutanen ne bayan samun korafi daga mazauna unguwar da gidan abincin yake a titin Lamido Crescent da ke cikin birnin na Kano, saboda yadda matsalar ke neman gurbata tarbiyar ya’yansu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wata kotun gwamnatin tarayya da ke Kano ta aike da wani mai sayar da magungunan jabu zuwa gidan yari na tsawoin shekaru uku, tare da biyan tarar naira 200,000.

Can ma a birnin Legas da ke Kudancin kasar NDLEA ta kama ƙwayar Tramadol sama da miliyan biyu da dubu dari bakwai, da aka yi yunkurin fita da ita kasashen waje daga tashar ruwan Apapa.

NDLEA ta ce kwayar na dauke ne a cikin katan-katan 55, da suka hada da nau’ukan Tapentadol da kuma Carisoprodol na Tramadol, da kudinsu ya kai naira miliyan daya da dubu dari uku da saba’in da biyar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending