News
An sake Sako mutane biyar da Yan bindiga sukayi garkuwa dasu a hanyar Kaduna da Abuja
Daga Muhammad Muhammad zahraddin da kabiru basiru fulatan
Yan bindigar da suka sace fasinjoji a jirgin kasar da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a Najeriya a watan Maris din da ya gabata sun saki karin fasinjoji biyar.
Hukumomin tsaro da gwamnatin kasar ba su tabbatar da sakin karin mutanen ba, amma BBC Hausa ta rawai to mutumin da ke shiga tsakani domin sako fasinjojin Tukur Mamu yana cewa an saki mutanen ne a yau Talata.
Ya bayyana cewa mutanen da aka saka su ne: Farfesa Mustapha Umar Imam, Akibu Lawal, Abubakar Ahmed Rufai, Mukthar Shu’aibu da Sidi Aminu Sharif.
Babu bayani kan ko sai da aka biya kudin fansa kafin a saki fasinjojin.
A watan jiya ne aka saki karin wasu fasinjojin jirgin kasan na Abuja-Kaduna kwanaki kadan bayan ‘yan bindigar sun fitar da wani bidiyo wanda ya nuna su suna lakada musu duka.
