Connect with us

News

An Kama Wani Matashi Dauke Da Kwayar Tramadol Mai Darajar Miliyan 25 A Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi nasarar cafke wani mutum mai suna Abba Musa mazaunin unguwar rijiyar zaki a jihar, dauke da kwayar Tramadol wadda darajarta ta kai naira miliyan 25.

 

Advertisement

Yan sandan sun kama Abba Musa ne dan kima I’m shekaru 30, dauke da fakitin Tramadol guda 500, da aka koda su a cikin motar da yake tunawa, akan titin Ahmadu Bello way, a ranar 31 ga watan Yuni da misalin karfe 10:30 na dare.

 

Advertisement

Jami’an Yan sandan caji ofis din Badawa ne suka yi nasarar kama matashin, wanda kuma bayan sun kama shi ya ce motar Ba yasa bace, don shima aikensa akayi da ita don da ya kaiwa wani a Yan Kaba.

 

Advertisement

 

Kwamitin Majalisar Dattawa Ya Yabawa NAF Bisa Tura Jiragen Super Tucano

Advertisement

 

 

Advertisement

Ƙwayar dai a bincike yan sandan sun gano cewa an shigo da ita Kano ne, daga Onitsha dake jihar Anambra.

 

Advertisement

Binciken da rundunar ta gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya bayyana cewa motar mallakin wani abokin sa ne mai suna Sulaiman Danwawu mazaunin unguwar Rijiyar Zaki ce.

 

Advertisement

 

A cewar sanarwa da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar rundunar ta yi nasarar kama mai motar, inda ya tabbatar da cewa ya tawo da kwayar ne daga Anambra domin siyar da ita a jihar Kano.

Advertisement

 

Jaridar indaranka cewa tuni dai mataimakin Kwamishinan ‘yan Sanda DCP Abubakar Zubairu ya bada umarnin ci gaba da bincikar lamarin.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending