Connect with us

Entertainment

Rayuwa ta na fuskantar barazana, Hadiza Gabon ta shaida wa kotu

Published

on

 

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Advertisement

 

 

Advertisement

Fitaccitar jarumar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon, ta yi ikirarin cewa rayuwarta na cikin haɗari saboda yadda ake fita da ita daga kotu a asirce a duk lokacin da aka zauna sauraron shari’arta.

Jarumar ta yi wannan bayani ne ta bakin lauyanta, Barista Mubarak Sani Jibril, a gaban wata kotun shari’ar Musulunci a Kaduna.

Advertisement

Lauyan na bukatar kotun ta yafe wa jarumar halartar zaman sauraron ƙarar da aka kai ta, tun da tana da wakilci.

Barista Mubarak ya ce taɓarɓarewar tsaro ya sa Hadiza Gabon cikin rashin kwaciyar hankali da fargabar abin da ka iya faruwa da rayuwarta idan ta ci gaba da halartar zaman kotun.

Advertisement

Radio Nigeria Kaduna ta rawaito lauyan yaci gaba da cewar duk lokacin da Gabon ta halarci zaman kotun, sai dai a yi satar fita da ita.

“Rayuwata na cikin hadari, rayuwar mai karar ma na cikin hadari. Ba mu san wa ke bibiyar wannan sharia’ar ba a kafofin sada zamunta ba.

Advertisement

“Idan ba a yi hankali ba za mu iya ganin mutane dauke da bindigogi domin su sace mu.

“Wannan ita ce damuwarmu ba wannan shari’ar ba,” in ji Barista Mubarak Sani Jibril

Advertisement

Lauyan mai kara, Barista Naira Murtala, ya ki yarda da rokon lauyan jarumar, yana mai ikirarin cewa dole ne ta ci gaba da halartar zaman kotu.

Alkali Rilwanu Kyaudai, ya tabbatar musu da cewa kotun za ta yi la’akari da lafiyar mai kara da wacce a ke kara a zamanta na gaba.

Advertisement

Hadiza Gabon ta halarci zaman kotun ne a ci gaba da sauraron karar da wani ma’aikacin gwamnati mai suna Bala Musa ya kai karar ta a bisa zargin ta ki ta aure shi bayan ya kashe mata kudi Naira 396,000.

Sai dai kuma Gabon ta shaida wa kotu cewa ba ta ma san mutumin da ke wannan iƙirari ba.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending