News
Tsawa ta faɗo tare da raunata mutum hudu a kusa da Fadar White House ta Amurka
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Maza biyu da mata biyu ne a filin shakatawa na Lafayette da ke birnin Washington DC suka ji munanan raunuka bayan mamakon ruwan sama da kuma faduwar tsawa, a cewar jami’an kwana-kwana.
Saboda kusancin filin da fadar shugaban Amurka, jami’an kare lafiyar shugaban kasa na secret service suna daga cikin mutane na farko da suka kai wa mutanen da walkiyar ta raunata ɗauki.
Nancy Pelosi ta ce Amurka ba za ta yarda China ta hantari Taiwan ba
Ba a tabbatar da sunayen wadanda suka ji rauni ba.
Tsawar ta faɗa a kan mutane huɗun ne a kusa da bishiya a gefen wani bango da ya kewaye Fadar White House a yammacin jiya.
BBC NEWS
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
