News
Goodluck Jonathan yana sa ido kan yadda zaɓen Kenya ke tafiya
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Tsohon shugaban kasar Najeriya na Goodluck Ebele Jonathan ya je kasar Kenya domin sa ido kan yadda zaben kasar ke gudana.
Mr Jonathan ya je ƙasar ne a karkashin inuwar wata kungiyar lura da zabe da manazartan dauwamammiyar dimokradiyya a Afirka (EISA), a matsayin dan kungiyar, domin gani-da-ido na yadda zabe ke tafiya a wasu mazaɓu a birnin Nairobi da ke Kenya.
Hankalin al’ummar yankin gabashin Afirka ya koma kan zaɓen Kenya
Shugaban ya bayyana manufar ziyarar a shafinsa na Facebook da cewa “yayin da mutanen Kenya suka fito yau domin jefa kuri’a a duk faɗin ƙasar, muna sa ran za a fito da sakamakon zaɓe lafiya da kuma karfafa dimokradiyyar ƙasar Kenya.
BBC NEWS
Advertisements
