Kafofin yaɗa labaran yankin gabashin Afirka sun gabatar da rahotanni na musamman akan zaɓen kasar Kenya, suna jaddada muhimmancin magajin Uhuru Kenyatta a siyasar yankin.
Jaridar Mwananchi mai amfani da harshen Swahili a Tanzaniya, ta buga labari a shafinta na farko dangane da korar jami’an zaɓe guda hudu da hukumar zaɓen kasar ta yi saboda sun haɗu da ƴan takara.
Ana satar ganga 400,000 na ɗanyen fetur a kowace rana a Najeriya-Gwamnatin taraiya
Jiya Litinin ne ta wallafa zanen barƙwanci a shafinta na farko mai taken “Sa’a 24 mai zafi a Kenya” wanda ya nuna ƴan takarar shugaban kasa guda huɗu suna kokawar shiga fadar gwamnati.
Jarida mai suna The Citizen, takwarar jaridar Mwananchi ta buga labari a shafinta na farko mai taken: “Abun da ƴan Kenya za su jefa wa ƙuri’a a zaɓen yau”, ɗauke da banbanci tsakanin manufofin ƴan takarar shugabannin ƙasa William Ruto da Raila Odinga.
