News
Ganduje ya aikawa majalisa ƙarin sunan mutum don tantacewa a matsayin Kwamishina
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya miƙa ƙarin sunan mutum ɗaya, wani, Ali Musa Burum-burum ga Majalisar Dokokin Kano- domin tantancewa a matsayin Kwamishina.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a jiya ne dai Ganduje ya aika da sunayen mutane 8 zuwa ga majalisar domin tantancewa a matsayin kwamishinoni don maye guraben waɗanda su ka yi murabus domin tsaya wa takara.
Babban Sakataren yaɗa labaran Majalisar, Uba Abdullahi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.
Yace karin sunan na ɗauke ne cikin wata wasiƙa da gwamnan ya aike wa Shugaban majalisar, Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari.
Sanarwar ta ce ana sa ran Ali Musa Burum-burum zai kasance cikin mutane 8 da Majalisar ta bukaci suje majalisar a mako mai zuwa domin tantance wa.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
