News
Gwamnatin tarayya ba,ashirye takeba cewar ASUU
Daga Yasir sani Abdullahi
Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya, ASUU, ta ce matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na ƙin biyan su albashi na lokacin yajin aiki zai ƙara dagula lamurra ne kawai a tattaunawar da suke yi.
Gwamnatin tarayya ta ce ba za ta biya malaman jami’o’in albashi ba na tsawon lokacin da suka shafe suna yajin aiki bayan sun shafe kusan wata shida ba sa aiki.
Sai dai ASUU ta ce wannan matakin zai kara dagula halin da ake ciki ne kawai.
Farfesa Abdulkadir Muhammad, shugaban kungiyar ASUU reshen Jihar Kano, ya yi karin bayani, yana mai cewa “gwamnati ba da gaske take ba”.
Kuma anjiyo kalaman ministan ilimi adamu adamu Yana cewa kungiyar Malaman Jami,oi sun batawa ɗalubai lokaci adan haka Yana shawartar su dasu bawa ɗalubai hakuri Kuma yace laifin ma ASUU ne
