Connect with us

News

Zamu bankado barayi masu satar Mai Kuma za,a hukun ta,su cewar garba shehu

Published

on

Garba shehu

Daga Yasir sani Abdullahi

Zamu ban kado barayin Mai na kasa kuma za,a hukun ta su dai dai da abinda suka aikata  cewar malam garba shehu

Mai magana da yawun shugaban kasa a Najeriya, Malam Garba Shehu, ya ce gwamnati na gab da bankaɗo sunayen manyan mutanen da ke da hannu dumu-dumu a harkar satar man fetur a Najeriya.

Malam Garba Shehu da ke waɗannan kalamai a wata hira da aka yi da shi a tashar Trust TV ta Najeriya, ya ce wannan wani ɓangare ne na irin kokarin da suke yi wajen kawo karshen mutanen da ke yi wa tattalin arziki zagon-kasa.

Ya ce abin kunya ne a ce Najeriya ta kasa cimma adadin da OPEC ta ba ta na danyen man da za ta iya fitarwa, saboda san rai na wasu mutanen.

Ya shaida yada aka ɗau tsawon lokacin domin samun irin wannan dama, amma yau a ce sun gaggara fitar da adadin man da ake bukata, abin kunya ne, in ji Garba Shehu.

Malam Garba ya ce jami’an tsaro sun yi kokari wajen ganin sun shawo kan matsalar. Kuma nan da ‘yan kwanaki kadan za su fitar da sunayen mutanen da ke aikata wannan muggan ayyuka

Advertisement

source of BBC

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending