News
Wayar salula ta yi sanadin ƙonewar gidan mai ƙurmus a Legas
Daga: Ibrahim Usman ijaiye
Hukumar ƴan kwana-kwana ta Jihar Legas ta ce a ranar Litinin, wani mutum ya sami raunuka bayan da wani abu ya fashe a wani gidan mai mai zaman kansa da ke garin Badagry na jihar.
Babban jami’i da ke kula da reashen hukumar ta Badagry Abel Husu ne ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya aukuwar wannan iftila’in.
ya ce hukumar tasu ta sami labarin abin da ke aukuwa ne a gidan man Yemoral Oil and Gas Petrol Station da ke kan hanyar Ajara a Badagry da misalin karfe 8:55 na ranar ta Litinin.
Ya ce jami’ansa sun isa gidan man bayan minti 10 da sami rahoton, kuma nan take suka fara kokarin kashe gobarar.
“Bincikenmu ya tabbatar cewa wani direban mota ne ya haddasa gobarar, bayan da ya riga ya sayi man fetur a cikin motarsa”.
Ya kuma ce “bayan da mai motar ya tayar da injin motar sai ta yi bindiga, inda gobara ta tashi nan take”.
Sai dai ma’aikata a gidan man sun shaida wa NAN cewa wani mutum ne ya yi sanadin gobarar bayan da ya amsa wayarsa a daidai lokacin da ake zuba ma sa fetur cikin wata jarka.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
