Rundunar ‘yan sandan Jihar Edo da ke kudancin Najeriya ta kai samame tare da kama mutum 30 da ake zargi da aikata kashe-kashe a ƙungiyoyin asiri a jihar.
Mataimakiyar mai magana da yawun rundunar, Jennifer Iwegbu, ta faɗa cikin wata sanarwa cewa sun yi nasarar kama mutanen ne bayan sun samu bayanan sirri cewa ‘yan ƙungiyar asiri na gudanar da ayyuka a kan Titin Oho da ke Benin, babban birnin jihar ranar Alhamis.
Kungiyar Masu Yabon Mazon Allah (SAW) Na Kasa, Sun Baiwa Gwamnan Yobe Lambar Yabo
Ta ce bayan dakarunsu sun isa wurin ne suka tarar da gawar wani mutum da aka gano sunansa Taiwo Edigie mai shekara 40, an datse kan sa kuma aka jefar a gefen jikin.
Sanarwar ta ƙara da cewa an samu irin wannan rahoton a Titin Imuetiyan na wani mutum da ba a tantance ko wane ne ba da aka kashe a hare-haren ‘yan asirin, shi ma a ranar Alhamis.
Abin da ya sa ke nan aka ƙaddamar da samamen, in ji sanarwar, kuma bayan kammala bincike za a gurfanar da waɗanda aka samu da laifi a gaban kotu domin neman hukunci, a cewar Jennifer.
