News
Rushewar gini a Abuja ta kashe mutum biyu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rashewar da wani gini mai hawa biyu a Abuja a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja ya yi ta kashe mutum biyu tare da jikkata wasu, a cewar rahoton Channels TV.
Jami’an hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa, NEMA na ci gaba da gudanar da aikin ceto.
Najeriya ta sakar wa kamfanonin sufurin jiragen sama na waje kuɗinsu da ta riƙe
A cewar rundunar tsaron ‘yan ƙasa ta Civil Defense, ginin ya rufta ne da tsakar dare ranar Alhamis – washegarin Juma’a – a kan titin Hamza Abdullahi da ke yankin Kubwa.
Wani mazaunin unguwar ya ce an ceto wasu mutane da suka jikkata, inda kuma aka wuce da su zuwa asibiti.
Bayan faruwar lamarin, Ministan Abuja Muhammad Musa Bello ya kai ziyara wurin, inda ya bukaci a gudanar da bincike kan dogayen gine-ginen da ke unguwar domin sanin kwarinsu
