Connect with us

News

A karshe dai kotu ta ayyana Dan PRP ne sahihin da ya lashe zaben cike gurbi a jihar plateau.

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

 

 

 

 

Advertisement

 

Biyo bayan karar da dan takarar kujerar majalisar wakilan tarayya na jam’iyyar PRP a zaben cike gurbi na mazabar Jos ta Arewa/Bassa, a karshe dai kotu yanke hukunci cewa Muhammad Adam Alkali, sahihin Wanda ya lashe zaben.

 

A hukunci na yau juma’a da Alkalai ukun Justice Hope O. Ozoh. Da Khadi Usman Umar, da kuma Justice Zainab M. Bashir, su ka yan ke sakamakon karar da aka shigar shine ya baiwa jam’iyyar ta PRP nasara.

An kama ma’aikatan lafiya kan mutuwar jariri sabon haihuwa

Haka zalika hukunci na kotun kuma ya bada umarnin da gaggauta amshi takardan shedar lashe zaben da aka baiwa Hon Musa Agah, na jam’iyyar (PDP) a zaben cike gurbin na watan Fabrairu.

Advertisement

 

Idan za’a iya tunawa dai tun da farko Baturen zaɓen Yinka Oyerinde, ya ayyana Musa Agah na PDP cewa ya samu Kuri’u 40,343, yayin da shi kuma Muhammed Adam Alkali, na PRP ya samu 37,757 jumulla yayin da Abbey Aku na (APC) ya samu 26,111.

 

‘Yan ratara 11 ne dai su ka fafata a zaben cike gurbin na Ranar 26 Fabrairu sakamakon Rasuwar Dan Majalisar yankin mai ci, Haruna Maitalla na jam’iyyar APC bayan wani haɗarin mota a watan Apirilun 2021.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending