Connect with us

News

Abubuwa 20 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sheikh Dahiru Bauchi

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

 

 

 

A farkon watan Almuharram ne fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, kuma jigo a Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya cika shekara 98 a duniya.

Advertisement

Baya ga tarin iliminsa da yawan shekaru, akwai wasu tarin baiwa da Allah Ya ba malamin, wadanda ba kowa ne ya san da su ba.

 

Aminiya ta yi nazari a kansu, inda ta zakulo muku abubuwa 18 da ya kamata ku sani a kansa.

Ga wasu daga ciki:

Ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a duniya, inda yake da ’ya’ya da jikoki da tataba-kunne kusan 300 da suka haddace Alkur’ani mai girma
Kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, ya ba shi shaidar girmamawa saboda yawan zuri’a mahaddata
Yana da ’ya’ya 95
Yana da jikoki 406
Yana da tattaba-kunne 100
’Ya’yansa mahaddata Alkur’ani 77
Jikokinsa mahaddata Alkur’ani 199
Tattaba-kunnensa mahaddata Alkur’ani 12
Shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Koli da ke bayar da fatawa a addinin Musulunci a Najeriya
An haife shi a watan Janairun 1927, wanda ya yi daidai da watan Muharram 1346 Bayan Hijira
A ranar Laraba aka haife shi a a garin Nafada da ke Jihar Gombe a yanzu
Kwararre ne a fannin Alkur’ani da Tafsiri da Ma’arifa da Hadisi da Harshen Larabci da Li’irabi da Fikihu
Jami’ar Tarayya da ke Lafiya a Jihar Nasarawa ta ba shi Digirin girmamawa
Gwamnatin Najeriya ta ba shi lambar girmamawa ta kasa ta OFR
Ya musuluntar da dubban mutane
Yakan yi saukar Alkur’ani duk bayan kwana biyu
Mutane fiye da 140,924 suka haddace Alkur’ani a makarantunsa da ke fadin Najeriya
Ya kafa makarantun haddar Alkur’ani sama da 1,500 a Najeriya da wasu kasashen Afirka
Karkashin gidauniyasa, an gina dakunan karatu guda 133,060 a Arewacin Najeriya
Ya shafe shekaru sama da 50 yana gabatar da tafsirin Alkur’ani a cikin watan Ramadan

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending