News
Hukumar EFCC Za Ta Daukaka Kara Kan Hukuncin Sakin Tsohon Gwamna
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin da mai shari’a C.L Dabup na babbar kotun jihar Filato ya yanke tare da wanke tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, da tsohon mai karbar kudi a ofishin sakataren gwamnatin jihar Yusuf Pam.
Mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren ya shaida wa Daily trust cewa hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta fara shirin daukaka kara a kan zargin damfara da ake yi wa jami’an gwamnatin biyu.
Har ila yau, darajar Naira ta ragu a kasuwar canji
Daily Trust ta ruwaito cewa, babbar kotun jihar Filato da ke zamanta a Jos a ranar Juma’ar nan ta sallami mutanen biyu tare da wanke su bisa wasu tuhume-tuhume 17 da suka hada da zamba cikin aminci da kuma karkatar da kudaden jihar Filato har Naira biliyan 6.3.
Daga cikin tuhume-tuhume kan zargin karkatar da naira biliyan biyu da babban bankin Najeriya (CBN) ya bayar domin karfafawa matasa da mata kanana da matsakaitan sana’o’i da kuma karkatar da kudaden da aka tanada domin koyarwa a makarantun gaba da sakandare (SUBEB).
Kotun ta kuma yi fatali da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon Gwamnan da kuma mai karbar kudin gwamnati, inda ta ce ba ta cancanta ba.
