Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallacin Juma’a a Zamfara, Sun Kwashe Jama’a

Published

on

DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Yan bindiga sun sace masallata masu tarin yawa daga Masallacin Juma’a na yankin Zugu dake karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigan sun boye bidigoginsu a cikin kayansu kuma suka shiga masallacin yayin da liman yake dab da fara huduba a jiya juma’a.

Advertisement

Maharan sun sanar da wadanda ke wajen Masallacin da su shiga ciki.

Hukumar EFCC Za Ta Daukaka Kara Kan Hukuncin Sakin Tsohon Gwamna

Advertisement

“A lokacin da suka zagaye masallacin, sun bukaci duk wadanda ke wajen masallacin da su shiga ciki cewa sun zo ne domin tattauna kan yadda zasu sako wasu mutanen dake hannunsu.

Wani mazaunin yankin ya ce

Advertisement

Babu wanda ya gansu da bindigogi kuma mutane da yawa sun kallesu a matsayin masallata.

Babu wanda ya mayar da hankali kansu saboda sun boye bindigoginsu.

Advertisement

“Sai dai, jim kadan bayan sun shiga cikin masallacin suka fito da bindigoginsu tare da yin harbin gargadi.

“Sun jagoranci masallata zuwa cikin daji amma wasu sun yi nasarar arcewa daga masallacin.

Advertisement

A cewar wata majiya, an sace Ladan, amma Liman ya sha da kyar.

Wasu daga cikin wadanda ke wajen masallacin duk an yi garkuwa da su saboda basu san ‘yan bindigan sun tsaya a wurare daban-daban a wajen masallacin ba.

Advertisement

Sun yi harbe-harbe a iska sannan suka tarkata jama’a zuwa daji.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, yace har yanzu bai samu rahoton farmakin ba amma ya yi alawakrin karin bayani idan ya samu daga bisani.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

LIBERTY NEWS

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending