Sports
Marcelo ya koma Olympiakos bayan shekara 15 a Real Madrid
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADINNI
Dan kasar Brazil mai tsaron baya Marcelo ya koma taka leda a kungiyar Girka, Olympiakos bayan barin Real Madrid a karshen kakar da ta wuce.
Mai shekara 34 ya bar Real Madrid a matakin wanda ke kan gaba a yawan lashe kofuna a tarihin kungiyar, bayan kaka 15 da ya yi.
Ya lashe La Liga na shida da Champions League na biyar a kakar da ta wuce, wadda ya buga karawa 18.
An bayar da rahoton cewar ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka daya a Olympiakos da cewar za a iya tsawaita idan ya taka rawar gani.
Kungiyar tana ta uku a kan teburin gasar Girka ta Greek Super League bayan wasa biyu da fara kakar nan.
Marcelo, wanda ya yi wa Real Madrid wasa 546, ya buga wa tawagar Brazil karawa 58, wadda ya fara taka mata leda a 2006.
Advertisements
