Connect with us

Sports

Serena Williams ta yi ban kwana da wasan Tennis

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

An cire tauraruwar wasa Serena Williams daga gasar Tennis ta US Open, abin da ke nufin ta buga babban wasan karshe a tarihi.

Advertisement

 

Ajla Tomljanovic ‘yar Australia ce ta doke ta a zagaye uku da suka buga a birnin New York na Amurka.

Advertisement

2023: Sha’aban Sharada Zai Ayyana Neman Kujerar Gwamnan Kano a Yau

Cikin hawaye, Serena ta gode wa iyalinta bisa goyon bayan da suka nuna mata tsawon shekaru.

Advertisement

 

Da ma a watan da ya gabata Ms Williams mai shekara 40 ta sanar da cewa gasar US Open za ta zama ta karshe kafin ta yi ritaya daga wasan Tennis.

Advertisement

 

“Ina matukar godiya a gare ku saboda ku kuka kawo ni nan,” in ji ta.

Advertisement

 

Serena Williams ta ci manyan kofunan Tennis na Grand Slams 23 a tarihi tun daga 1999 da ta ɗauki na farko

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending