News
Wuta Ta Kona Gine-gine Yayin Da Tankar mai Ta Fashe
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kimanin gine-gine 10 ne suka kone kurmus bayan da wata tankar da ke dauke da kaya ta fado kuma ta fashe a kan iyakar Olambe da Matogun da ke karamar hukumar Ifo ta jihar Ogun ranar Asabar.
Ko’odinetan hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa Ibrahim Farinloye, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar ya ce ba a samu asarar rayuka ba.
Jam’iyyar ADC a Najeriya ta dakatar da ɗan takararta na shugaban ƙasa
Farinloye ya ce, “Wata tankar mai dauke da kimanin lita 45,000 na PMS ta yi hatsari, ta zubar da abin da ke cikinta sannan ta fashe da misalin karfe 7 na safe a Olambe, kan titin Matogun, a karamar hukumar Ifo, jihar Ogun.
“Duk da cewa babu wani rai da aka rasa ko kuma wani ya samu rauni amma kusan gine-gine 10 ne suka cinye a lamarin.”
A halin yanzu dai an kashe wutar.
PUNCH
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
