Hukumar da ke yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce ƙarin mutum 173 sun kamu da cutar korona tsakanin Alhamis da Juma’a a ƙasar.
Alƙaluman da hukumar ta fitar a yau Asabar sun bayyana cewa Jihar Legas ce kan gaba da sabbin kamuwar 79, sai Kano da ke biye mata da 39, da kuma Rivers mai 27.
Ƴan Sanda sun kama matar da ta shirya aka yi garkuwa da mijinta
Sauran su ne: Kaduna-14, Delta-4, Filato-4, Abia-3, Kwara-2, Taraba-1.
Ya zuwa yanzu, jimillar mutum 263,867 ne aka tabbatar sun kamu da cutar, sannan ta kashe 3,148 tun bayan ɓullarta a Fabarairun 2020.
