Connect with us

News

Yan Sanda Sun Yi Gumurzu da Yan Bindiga, Sun Ceto Dan Takarar PDP a Katsina.

Published

on

Yan sanda

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

 

 

Advertisement

 

Dakarun rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina, sun kuɓutar da ɗan takarar majalisar jiha mai wakiltar Kankiya a inuwar PDP, Ibrahim Tafashiya, daga hannun ‘yan ta’adda.

 

Rahotanni sun ce tun da farko a daren ranar asabar, ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da Tafashiya a yankin ƙaramar hukumar Kankiya.

APC: Machina ya musanta janyewa daga takarar Sanatan Yobe ta Arewa

Bayan sanar da ‘yan sanda lamarin garkuwan, nan take DPO na caji Ofis ɗin Kankiya, SP Iliyasu Ibrahim da ‘yan tawagarsa suka toshe hanyar fitar maharan, suka yi ɗauki-ba-daɗi da su har suka samu nasarar ceto ɗan takarar.

Advertisement

 

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da wannan nasara a jiya Lahadi.

 

Wasu rahotanni sun nuna cewa ‘yan ta’adda sun shiga gidan Rijistaran kwalejin ilimi ta tuna wa da Isah Kaita (IKCOE), Salisu Gide, dake cikin garin Kankiya, inda suka sace shi da matarsa.

 

Dakarun ‘yan sandan sun yi nasarar ceto Giɗe, yayin da suke cigaba da kokarin ceto matarsa da sauran mutanen da maharan suka tattara a harin. Kakakin ‘yan sanda ya ƙara da bayanin cewa an ga ‘yan ta’adda a wani wuri dake yankin ƙaramar hukumar Batsari, cikin jihar Katsina.

Advertisement

 

Sannu a hankali dai hare haren ƴan bindiga na ƙarasowa garin na Kankiya, wanda ke kan hanyar Kano zuwa Katsina.

 

Mutane da dama mazauna ƙauyukan da ke ƙaramar hukumar Kurfi sun tsere daga gidajen su, sun dawo garin na Kankiya.

 

Masana harkokin tsaro sun yi gargadin cewa, idan har hare haren ƴan bindiga ya ɗore a garin na Kankiya, toh lallai zai yi barazana ga dubban matafiyan da sintiri daga Kano zuwa birnin Katsina.

Advertisement

 

 

 

LIBERTY NEWS

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending