Kungiyar Jama’atul Kitabu Was-sunnah a Jamhuriyar Nijar ta fara wani zama na kwanaki bakwai da zummar karawa juna sani tsakanin malamai, da ba su horo kan dabarun yin wa’azi ba tare da amfani da kalamai ko lafuzan da ka iya ta da zaune tsaye ba.
Malaman da kungiyar ta gayyato daga wurare daban-daban, za su bai wa malaman jihohi 8 wannan horo, da nufin tsaftace harkokin wa’azi da abin da yta shafi addini a kasar.
Kungiyar Kitabu Was-sunna na aikin na hadin gwiwa tsakaninta da ofishin ministan cikin gida, manufar ita ce magance tsattsauran ra’ayin addfinin Islama, da kaucewa kalaman batanci ga addinin.
Ƙungiyar tallafa wa ilimin ƴaƴa mata ta yaba wa Ganduje bisa ɗaukar malamai mata 195 aiki
Malaman Abdussamad Yahaya shi ne daraktan harkokin addinai a ofishin ministan cikin gida a jamhuriyar Nijar, ya shaida wa BBC cewa: ”Horas da malamai dangane da abin da ya shafi harkokin addfini yana da muhimmanci, da tabbatar da zaman lafiya, saboda mun lura malaman da ke wa’azi ko aikewa da sako da wadanda ke Khuduba a ranar Juma’a, suna bukatar sanin makamar abin da suke yadawa domin kauce wa ta da hankali.”
Ana yawan korafi kan yadda wasu malamai ke zafafawa ko fadar abin da ya zo bakunansu lokutan wa’azi, inda kan tunzura mabiya har a samu barkewar tashin hankali tsakanin mabiya addinai daban-daban, ko ma wadanda ke cikin addinin guda.
