Connect with us

News

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Zaria

Published

on

Advertisements
ads

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

 

 

 

 

 

 

Advertisement

 

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da fatattakar ‘yan bindiga a yankin Fondisho da ke karamar hukumar Igabi kan hanyar Kaduna zuwa Zaria a arewacin kasar.

Wata sanarwa da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Laraba ta ce sojojin sun samu kwararan bayanan sirri kan maboyar ‘yan bindigar, kuma ba tare da bata lokaci ba suka yi musu kwanton bauna.

Sai dai ‘yan bindigar sun yi kokarin fantsama cikin daji, amma hakan ba ta samu ba sakamakon bude wutar da jami’an tsaron Najeriyar suka yi.

Ayarin motocin dakon kaya dauke da hatsi sun isa Habasha daga Ukraine

Sojojin sun yi nasarar kashe biyu daga cikin ‘yan bindigar, sun kuma kwace makamai kamar bindiga da alburusai, har da tsabar kudi.

Advertisement

Sanarwar ta ci gaba da cewa, jami’an tsaro za su ci gaba da yin sintiri a yankin har sai sun tabbatar da kakkabe ‘yan bindigar da suka hana jihar Kaduna da jihohi makwabta sakat wajen satar mutane domin neman kudin fansa.

BBC NEWS

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending