Connect with us

News

Ayarin motocin dakon kaya dauke da hatsi sun isa Habasha daga Ukraine

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Manyan motocin dakon kaya guda 60 dauke da hatsi daga Ukraine sun isa Habasha kusan wata guda bayan barin tashar jiragen ruwa ta Bahrul Aswad a Pivdennyi.

 

Advertisement

Shirin samar da abinci na duniya ne ya sayo kayan abincin domin taimaka wa a kasar da ke kusurwar Afirka.

 

Advertisement

Wannan ne jirage na farko da suka dauki hatsi daga Ukraine zuwa Afirka tun bayan mamayar kasar da Rasha ta yi.

Babban tafkin Pakistan da ke barazanar ballewa ya fara raguwa

Advertisement

Shirin samar da abincin na duniya sun fadawa BBC cewa kayan abincin zai taimaka wajen ciyar da mutane kusan sama da miliyan daya da rabi na tsawon wata daya.

 

Advertisement

Habasha hade da wasu kasashe a yankin, na fama da mummunan fari na tsawon lokaci, inda fada a yankin arewacin Tigray da ake ci gaba da yi, ya jefa mutane miliyan 20 cikin bukatar agajin gaggawa na abinci.

 

Advertisement

Sai dai sake barkewwar fada a arewacin kasar, na nufin cewa kai kayan abinci inda ake so na da matukar wahala – musamman a yankin Tigray da ake gwabza fada.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending