Connect with us

News

Ana son dakatar da shugabannin kananan hukumomi 15 a jihar Naija .

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Wani kwamiti da majalisar dokokin jihar Naija ya kafa domin bincike game da bashin kudin kwangilar da aka bai wa kananan hukumomin jihar 25, ya bukaci da a dakatar da shugabannin kananan hukumomi 15 a fadin jihar.

Advertisement

Gidan Talabijin na Channels Tv a Najeriya ya ruwaito shugaban kwamitin Abdulmalik Madaki Bosso, na cewa matakin zai bayar da dama ga mambobin kwamitin domin gudanar da aikinsu na bincike kamar yadda ya kamata.

Ƴan bindiga sun kashe malamin addinin Muslunci a Ebonyi

Advertisement

A yayin da yake jawabi ga majalisar dokokin jihar shugaban kwamitin, Abdulmalik Madaki Bosso, ya ce kananan hukumin da kwamitin ke son a dakatar sun hadar da Mokwa, da Gbako, da Suleja, da Gurara, da Tafa Paikoro, da Bosso, da Agwara, da Borgu, da Kontagora, da Wushishi, da Magama, da Mariga, da Mashegu, da kuma Rijau.

Mista Bosso ya yi zargin cewa mafiya yawan shugabannin da aka dakatar sun karbi bashin ne ba tare da bin ka’idojin da ya ce majalisar dokokin jihar ba za ta lamunta ba.

Advertisement

BBC NEWS

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending