News
2023: NNPP na neman INEC ta soke takarar gwamna da ta ɗan majalisar jiha a Kaduna
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Jam’iyyar NNPP mai kayan marmari, ta maka Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, a gaban Mai Shari’a Hadiza Shagari ta wata babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kaduna.
Jam’iyyar na ƙalubalantar jerin sunayen jam’iyyar APC, ƴan takarar kujerar gwamna da na majalisar jiha da INEC ta wallafa a ranar 22 ga watan Yuli, domin gudanar da babban zaɓe.
Kyandar Biri: Najeriya Ce Tafi Yawan Matattu Da Kamuwa Da Cutar A Afirka–WHO
Jam’iyyar NNPP ta yi zargin cewa ƴan takarar ba su fito ta hanyar doka ko kuma ƙa’ida ba kamar yadda dokar zaɓe da sauran wasu dokoki suka tanada ba.
Don haka jam’iyyar ta buƙaci kotu da ta tilasta wa INEC yin abin da ya dace ta hanyar cire ƴan takarar jam’iyyar APC daga jerin sunayen ƴan takarar da suka cancanta a zaben 2023 a jihar Kaduna.
Shari’a,r wacce aka fara karanta ta a Kaduna a yau Juma’a, an dage ci gaba da sauraren ta zuwa ranar 15 ga watan Satumba.
Mai shari’a Hadiza ta bayyana cewa, an ɗage shari’ar ne bisa hujjar cewa har yanzu INEC ba ta kai wa dukkan ɓangarorin biyu kwafi na takardu domin samun bayanai ba.
DAILY NIGERIAN
