An soke tare da ɗage harkokin wasanni a sassan Burtaniya sakamakon mutuwar Sarauniya Elizabeth ta biyu inda fitattu a ɓangaren wasanni ke ci gaba da karrama marigayiyar.
Gwarzon ɗan ƙwallon ƙafar nan ɗan Brazil, Pele ya ce Sarauniyar ta kasance tana burge shi tun bayan da ya fara haɗuwa da ita a 1968.
Anambra Ce Ta 5 Wajen Yada Cutar AIDS A Najeriya
Shi kuwa Roger Federer, gwarzon ɗan wasan Tennis na maza ya ce za a ci gaba da tunawa da ita tsawon rayuwa.
Hukumar kula da tseren doki ta Burtaniya ta dakatar da duk wata gasa tsakanin jiya Alhamis da yau Juma’a tare da cewa ana alhinin mutuwar Sarauniyar da ta damu da dawakai.
Kazalika an soke wasan ƙwallon cricket na maza tsakanin Ingila da Afirka ta Kudu da aka shirya yi a yau.
An kuma ɗage wasanni biyu na league ɗin Ingila da aka tsara bugawa a yau.
