Sports
Za a dawo da harkokin wasanni a Ingila ranar Talata
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
A gobe Talata ne za a dawo da wasannin gasar kasar Ingila, bayan da aka dakatar da harkokin wasanni saboda alhinin rasuwar Sarauniya Elizabeth II.
To sai dai za a yi shiru na minti daya a cikin filin tare da karanta taken kasa, gabanin fara wasa domin nuna alhini ga rasuwar Sarauniya.
Haka kuma ‘yan wasa za su daura bakin kambu, tare da sauko da tuta kasa-kasa
A karshen makon da ya kabata ne dai aka dakatar da harkokin wasanni a kasashen Ingila da Wales, da Scotland da kuma Ireland ta arewa, sakamakon rasuwar sarauniya Elizabeth II.
Advertisements
