Sports
Lewandowski zai fuskanci Bayern Munich
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kociyan Bayern Munich, Julian Nagelsmann ya ce ya kagu ya sake haduwa da Robert Lewandowski, bayan da za su fafata da Barcelona a Champions League.
Kungiyoyin biyu za su fafata a gasar Zakarun Turai ranar Talata wasa na biyu a rukuni na uku.
Sai Shugabanni Sun Yi Adalci, Talaka Ya Gyara Hali, Najeriya Za Ta Zauna Lafiya -Kwararru
Ranar 7 ga watan Satumba, Bayern Munich ta je Italiya ta doke Inter Milan da ci 2-0 a wasan farko a rukuni na ukun.
Ita kuwa Barcelona a Camp Nou ta ci FC Viktoria Plzen 5-1, kuma Robert Lewandowski ne ya ci mata uku a karawar.
Ya kafa tarihin cin uku rigis a Champions League a kungiya uku har da Bayern Munich da Borussia Dortmund.
Wannan shi ne wasa na 14 da za su kara a Gasar Zakarun Turai, inda Bayern ta ci tara, Barca ta yi
Barcelona ta dauki Robert Lewandowski daga Bayern Munich kan yarjejeniyar kaka hudu kan fam miliyan 42.6 a bana.
Mai shekara 33 yana da saura kwantiragin kaka daya a Bayern Munich, sai dai a watan Mayu ya sanar cewar yana son ya koma wata kungiyar.
Nan da nan dan kwallon ya kasance da ‘yan wasan Barcelona a Amurka, wadda ta shirya yin wasan sada zumunta hudu, domin tunkarar kakar tamaula.
Barcelona ta gindaya fam miliyan 429.9 ga duk wadda za ta dauke Lewandowski idan yarjejeniyarsa bai kare ba a Camp Nou.
Lewandowski shi ne na hudu da Barcelona ta dauka a bana, bayan dan kwallon Brazil, Raphinha daga Leeds United da Franck Kessie da AC Milan da Andreas Christensen daga Chelsea.
Haka kuma Bayern ta sayi dan wasan tawagar Netherlands, Matthijs de Ligh daga Juventus kan yarjejeniyar kaka biyar kan fam miliyan 65.6.
Lewandowski mai shekara 34 ya ci kwallo tara a karawa shida da ya yi wa sabuwar kungiyarsa Barcelona a bana.
Lewandowski ya koma Bayern Munich da taka leda a 2014 a lokacin da yarjejeniyarsa ta kare a Borussia Dortmund.
A nuwambar 2013, Lewandowski ya tabbatar da zai bar Borussia Dortmund zuwa abokiyar hamayya Bayern Munich.
Ya koma Bayern ranar 3 ga watan Janairun 2014, wanda ya saka hannu kan kwantiragin kaka biyar a lokacin.
An gabatar da dan wasan a Bayern Munich ranar 9 ga watan Yulin 2014.
Lewandowski ya ci kwallo 50 a wasa 46 a kakar da ta wuce, ya kuma taimakawa Bayern ta dauki Bundesliga na 10 a jere.
Lewandowski ya zura kwallo 344 a raga a wasa 374 a Bayern, shi ne na biyu a tarihin cin kwallaye a kungiyar bayan Gerd Muller.
Dan wasan ya lashe German Bundesliga a kowacce kaka takwas da ya yi a Bayern Munich.
Ya kuma dauki Champions League a 2020 da kuma German Cups a kungiyar ta Jamus.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
