Sports
Bayern ta ci Barca karo na 10 a Gasar Zakarun Turai
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Bayern Munich ta ci wasa na biyu a jere a Champions League na bana, bayan da ta doke Barcelona ranar Talata a Jamus.
Kungiyoyin biyu sun kara a wasa na biyu a cikin rukuni a babbar gasar tamaula ta Zakarun Turai.
Sun kuma kammala minti 45 din farko ba tare da cin kwallo ba, haka suka je hutu.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Bayern ta zura kwallo a raga ta hannun Lucas Hernandez a minti na biyar da komawa taka leda.
Minti hudu tsakani Leroy Sane ya ci wa Bayern Munich kwallo na biyu da ya bai wa kungiyar Jamus maki ukun da take bukata.
Wannan shi ne karo na 14 da aka fafata tsakanin Bayern Munich da Barcelona a wasannin Zakarun Turai.
Kungiyar Jamus ta yi nasara a karo na 10, yayin da ta Sifaniya ta ci biyu da canjaras biyu.
Ranar 7 ga watan Satumba Barcelona ta dura 5-1 a ragar Victoria Polzen a Camp Nou a wasan farko na cikin rukuni a Champions League.
Jerin haduwa da aka yi tsakanin Bayern da Barca:
2022/23
Champions League Talata 13 ga watan Satumbar 2022
B Munich 2-0 Barcelona
2021/2022
Champions League Laraba 8 ga Disambar 2021
B Munich 3 – 0 Barcelona
Champions League Talata 14 ga watan Satumbar 2021
Barcelona 0 – 3 B Munich
2019/2020
Champions League Juma’a 14 ga watan Agustan 2020
Barcelona 2 – 8 B Munich
2014/2015
Champions League Talata 12 ga watan Mayun 2015
B Munich 3 – 2 Barcelona
Champions League Laraba 6 ga watan Mayun 2015
Barcelona 3 – 0 B Munich
2012/2013
Champions League Laraba 1 ga watan Mayun 2013
Barcelona 0 – 3 B Munich
Champions League Talata 23 ga watan Afirilun 2013
B Munich 4 – 0 Barcelona
2008/2009
Champions League Talata 14 ga watan Afirilun 2009
B Munich 1 – 1 Barcelona
Champions League Laraba 8 ga watan Afirilun 2009
Barcelona 4 – 0 B Munich
1998/1999
Champions League Laraba 4 ga watan Nuwambar 1998
Barcelona 1 – 2 B Munich
Champions League Laraba 21 ga watan Oktoban 1998
B Munich 1 – 0 Barcelona
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
