News
Na Fi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kaunar Najeria: Sheik Ahmad Gumi
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Fittaccen malamin addinin Islama Sheikh Ahmed Gumi ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ya kaunar Nigeria kamar yadda shi yake son ta.
Gumi ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani game da kama Tukur Mamu da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi.
A jawabinsa na mako-mako a masallacin Sultan Bello Kaduna, Gumi ya ce Mamu ya ce kamata ya yi gwamnati ta nemi gafara bisa zargin tursasa Mamu.
Zamanin baddala alƙaluman sakamakon zaɓe ya wuce -INEC
Ya ce shi da kansa ya dauki matakin kwantar da hankalin ‘yan bindiga domin a samu zaman lafiya, amma wasu ba sa son gaskiya.
“A matsayinmu na mutane, ba za mu iya naɗe hannayenmu ba muna yin komai. Na san waɗannan ayyukan tsaro saboda ni kaina ɗaya ne a cikin tsarin tsaro. Don haka, na san yadda suke aiki kuma na san makircinsu. Ko Sardauna bai kubuta daga makircin su ba, irin su Murtala, Maimalari, da IBB, har da shi kansa Buhari. Dukkansu sun fuskanci makircinsu.
“Kwanan nan su ma Malam Goni ya fada cikin makircin su; lokacin da wasu matasa sojoji suka kashe shi. To wa ke alfahari da su? Na yanke shawarar shiga wannan batu ne don taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar. Bari in gaya muku ko shugaban kasa baya kaunar kasar nan kamar yadda nake yi domin ba ni da wata kasa sai Najeriya.
“Ina son kasar nan ta kasance cikin kwanciyar hankali, shi ya sa na yi kasada da rayuwata na shiga dajin domin nemo mafita ga rashin tsaro. Amma wasu mutane ba sa son hakan ta faru. Ba su da sha’awar neman hanyar magance matsalar, domin sun fahimci cewa da gaske nake a kai, sai suka yanke shawarar a rika kirana da sunaye iri-iri, suna alakanta ni da ta’addanci.
“Abin da ya ba su haushi shi ne na ce wadannan mutanen sun cancanci ababen more rayuwa kamar asibitoci, makarantu kamar yadda aka yi wa tsagerun Neja Delta. Hakan ya janyo zagi.”
DAILY TRUST
