News
Yawan Ciwo Basussuka: Gode mana yakamata a yi, ba yawan ƙorafi ba – Buhari
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya na sane da yawan damuwar da ‘yan Najeriya ke nunawa, dangane da yawan basussuka da ake ciwowa.
Sai dai kuma ya ce ya kamata a gode saboda ana ciwo basussukan ne domin a yi ayyukan inganta ƙasa, raya ƙasa da kuma inganta rayuwar al’ummar ƙasa.
Saura Kiris Cutar Zazzabin Cizon Sauro Ta Zama Tarihi —Rahoto
Buhari ya yi wannan bayani lokacin da ya ke ƙaddamar da Kwamitin Shugaban Ƙasa Mai Lura da Tattalin Arzikin Ƙasa, a karshen makon nan a Abuja.
Buhari wanda yace an riƙa ciwo bashin ne tilas saboda halin da tattalin arzikin duniya da kuma matsalolin da Najeriya ta fuskanta, ya danganta matsalolin da korona, yaƙin Rasha da Ukraine, sai kuma raguwar ɗanyen man da Najeriya ke haƙowa a kullum.
Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada cewa duk da ƙalubalen da tattalin arzikin duniya ke fuskanta da kuma rigingimun cikin ƙasa, hakan bai hana tattalin Najeriya bunƙasa da ci gaba ba.
Buhari ya ce tattalin arzikin ƙasa gaba ya ke yi ba baya ba, yayin da ya ke jawabi wurin ƙaddamar da Kwamitin Shugaban Ƙasa Mai Bada Shawara kan Tattalin Arziki.
Buhari ya ce annobar korona da yaƙin Ukraine da Rasha da asarar ɗimbin ɗanyen man fetur, sun haifar wa tattalin arzikin Najeriya naƙasu sosai.
“Duniya ta yi fama da manyan ƙalubale a cikin shekaru ukun nan, tun daga kullen korona, wanda ya tsaida komai, kuma ya haifar da tashin gwauron zabin farashin kayan abinci da kayan masarufi a duniya.
“Sai kuma daidai lokacin da ake ƙoƙarin fita daga ƙuncin korona, yaƙi ya ɓarke tsakanin Rasha da Ukraniya, wadda ya haifar wa duniya wata babbar matsalar da har yau ake ƙoƙarin ganin an warware ta.
“Amma kuma duk da ƙalubalen da ake fuskanta, tattalin arzikin mu gaba ya ke ci ba baya ba.”
Buhari ya kuma yi magana a kan matsalar raguwar ɗanyen man da Najeriya ke haƙowa da ya ce a Agusta 2022 an riƙa haƙo ƙasa da ganga miliyan ɗaya.
Ire-iren waɗannan matsaloli inji Buhari ke haddasa tilas ake fita ranto kuɗaɗe domin aikata ayyukan inganta rayuwar al’umma.
Ya ce Gwamnatin sa zata ci gaba da inganta rayuwar al’umma musamman ta ƙarƙashin Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu (SIP).
Dangane da yawan ciwo bashin da gwamnatin sa ke yi, ya ce wannan ba abin damuwa ba ne, domin kuɗaɗen da ake ramtowa ana yin ayyukan raya ƙasa da raya al’umma ne da su, musamman ayyukan more rayuwa, inganta lafiya da sauran ayyukan inganta rayuwar masara galihu.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
