Connect with us

News

INEC Ta Soke Rajistar Zaben Mutum Miliyan 1.12

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta soke rajistar zaben mutum 1,126,359 daga cikin mutum 2,523,458 da suka yi rijistar zabe a karon farko daga watan yunin 2021 zuwa watan Janairun 2022.

Advertisement

 

Kwamishinan INEC na Kasa kan Yada Labarai da Wayar da Kai, Festus Okoye, ne ya sanar da haka, kafin wayewar garin Talata a Abuja.

Advertisement

Ambaliya Ta Raba Kwaltar Titin Bursari Zuwa Damaturu Gida Biyu a Jihar Yobe

Ya jaddada cewa INEC za ta fara rabon katunan zaben mutanen da suka yi rajista a karon farko da wadanda suka sabunta nasu a watan Oktoba da watan Nuwamba masu kamawa.

Advertisement

 

Festus Okoye ya ce tun ranar 31 ga watan Yuni da aka rufe yin rijistar masu zabe hukumar ta fara aikin tatancewa da kuma tsaftace rajistar zabe.

Advertisement

 

“Da farko INEC ta sanar cewa an sami mutum 2,523,458 da suka yi rajistar zabe a karon farko daga ranar 28 ga watan Yuni, 2021, zuwa 14 ga watan Janairu 2022.

Advertisement

 

“Sai dai kuma mutum 1,126,359 daga cikinsu rajistar da suka yi ba ta inganta ba, kuma an soke,” in ji Festus Okoye.

Advertisement

 

Hakan na nufin kawo yanzu karin mutum 1,397,099 aka samu a kan yawan masu zabe da ake da su a 2019 a Najeriya.

Advertisement

 

Okoye ya kara da cewa nan ba da jimawa ba hukumar za ta kammala aikin tantance wadanda suka yi rajistar zabe daga ranar 15 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Yuli, 2022, wadanda su ma a cikinsu aka gano mutane da yawa da suka yi rajista fiye da sau daya ko ba su cancanci yin rajista ba — kuma su ma an soka nasu.

Advertisement

 

Ya ce, “Wadanda hakan ta shafa sun hada da mutanen da suka saba ka’idojin hukumar, wadda ta ba da muhimmanci ga samun sahihin rajistar zabe domin tabbatar da gaskiya.

Advertisement

 

“Da zarar an kammala za a yi wa jama’a da bayani kamar yadda muka saba.

Advertisement

 

“Daga nan za a shigar da sabbin mutanen a tsohon rajistar da ake da ita, sannan a wallafa sunayen domin kowa ya gani, kamar yadda Sashe na19 (1) na Dokar Zabe ya 2022 ya tanada.”

Advertisement

 

Ya bayyana cewa hukumar na bin tsauraran matakai domin tabbatar da tsaftace rajistar da ke dauke da bayanan masu zabe.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY TRUST

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending