Connect with us

News

Minister ya bada umarnin maida rubuta jarrabawar ƙarin matsayi na hukumomin NIS, NSCDC zuwa jihohi

Published

on

Advertisements
ads

Minister ya bada umarnin maida rubuta jarrabawar ƙarin matsayi na hukumomin NIS, NSCDC zuwa jihohi

 

Ministan harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya bayar da umarnin a riƙa gudanar da jarabawar karin matsayi ga ma’aikatan Hukumar Shige-da-fice ta Ƙasa, NIS, da ta kashe gobara, da hukumar kare fararen hula, NSCDC da kuma hukumar kula da gidajen yari zuwa jihohi, maimakon Abuja kadai.

 

Ministan ya fadi hakan a jiya Talata, ya na mai cewa cibiyar da hukumomin ke amfani da ita wajen jarrabawar ta na da cunkoson jama’a, kuma hakan ba zai bayar da sakamakon da a ke buƙata ba.

TIRƘASHI: Kansila ya naɗa muƙamai 32 a Kaduna

Advertisement

Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Afonja Ajibola ya fitar, ta ce ministan ya ba da umarnin ne a lokacin da ya ziyarci Cibiyar Jarrabawa ta yanar gizo, CBT ta Saascon International School da ke Abuja.kamar yanda jaridar Daily Nigerian fa rawaito

 

Hukumar na amfani da wannan cibiya wajen gudanar da jarabawar karin girma ga hukumomi hudu da ke karkashinta.

 

Kakakin ma’aikatar ya ce Aregbesola ya lura cewa jarrabawar a cikin irin wannan yanayi mai cike da cunkoson jama’a ba zai ba wa tsarin mutuncin da ya dace ba.

 

Advertisement

Don haka ya umarci sakatariyar hukumar Aisha Rufa’i da ta gudanar da jarabawar karin girma a jihohi daban-daban na tarayya.

 

Aregbesola ya ce akwai cibiyoyi na CBT a fadin jihohin da za a yi amfani da su wajen gudanar da jarrabawar ba tare da wata matsala ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending