News
An kama mahaifin da ya kashe ‘Yarsa’ budurwa yayi tsafi da ita
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
‘Yan sanda sun kama wani mahaifi wanda ya kashe’yar sa’ ‘yar shekara 15 yayi tsafi da ita.Mutumin mai shekaru 50 mai suna Dauda Ibrahim mazaunin garin Idah a karamar hukumar ta Idah a jihar Kogi ya hada baki ne da wasu mutane biyu suka sace ‘yar tashi mai suna Sherifah suka kasheta sannan suka cire wasu sassa na jikinta suka yi tsafi dashi
Minister ya bada umarnin maida rubuta jarrabawar ƙarin matsayi na hukumomin NIS, NSCDC zuwa jihohi
Rahoton’yan sanda ya nuna cewa mutumin ma’aikaci ne na Kwalejin fasaha ta gwamnatin tarayya dake garin Idah a jihar ta Kogi (Federal Polytechnic, Idah)
Bayanai sun ce a ranar 4 ga watan jiya na Agusta ne mutanen biyu bisa umarnin mahaifin marigayiya Sherifah suka je gidansu dake unguwar Okenya akan titin Itayi dake yankin karamar hukumar Igalamela/Idolu suka saceta .
An Kuma gano gawarta ne a cikin wani kabari da mutanen suka haka bayan sun kasheta, sannan an cire wasu sassa na ganfan jikinta.
Gaskiya Tafi kobo
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
