A ranar Litinin ne aka yankewa wani mai garkuwa da mutane, Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, da wanda ake karansa, Victor Aduba, hukuncin daurin shekaru 21 a gidan yari. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
Ya Datse Hannun Wani Saboda Ya Zagar Masa Budurwa
Mai shari’a Oluwatoyin Taiwo na kotun hukunta manyan laifuka ta Ikeja da ke jihar Legas ne ya yanke hukuncin.
Wadanda aka yanke wa hukuncin, an zarge su ne da hada baki da kuma yin garkuwa da Sylvanus Ahanonu Hafia a ranar 23 ga watan Yunin shwkarar 2014, a hanayar Kara Street dake yankjn Amuwo Odofin na Legas.
Ana zargin sun kama Hafia tare da tsare shi kuma sun nemi a biya su kudin fansan dayakai dalar Amurika Milliyan 2.
