News
Ƙungiyar ASUU za ta ɗaukaka ƙarar hukuncin da kotu ta yanke na ta janye yajin aiki
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADEEN
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU ta shirya daukaka kara kan umarnin da kotun masana’antu ta bata na dakatar da yajin aikin da ta kwashe watanni Bakwai tana yi.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar shiyyar Lagos, Mr Adelaja Odukoya, yace kungiyar ta bukaci Yayanta da su kwantar da hankalinsu akan umarnin Kotun Kuma su jira mataki na gaba
Sanatoci sun yi shiru kan tsige Buhari
Kungiyar ta ce tuni lauyanta ya shigar da kara akokarin bin kadin wannan umarni.
Sanarwar tace; “Ku kwantar da hankalinku.” Ta kuma bukaci mambobin kungiyar da ‘yan Najeriya da su kasance masu hadin kai, duk da cewa za a janye wannan umarni.
Sanarwar ta kara da cewa; “Shugaban kungiyarmu, Kwamared Victor Osodeke, ya bukaci mambobin kungiyarmu ta kasa da su kwantar da hankalinsu domin babu wani abin damuwa a bayan aiki da aka gabatar a yau.
“Lauyan mu ya shigar da kara dan dakatar da aiwatar da wannan hukuncin. Ba za a taɓa yin galaba a kan jama’ar da ke haɗin kai ba tare da sulhu ba.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
