Connect with us

News

Najeriya ba za ta wargaje ba

Published

on

DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAHI

Tsohon shugaba kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) ya shawarci al’ummar kasar su zama masu kwarin gwiwa da kyakkyawan fata duk da matsalolin da Najeriya take ciki.

Najeriya in ji shi, za ta ci gaba da kasancewa dunkulalliyar kasa guda.

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wani yaro bayan an yi masa allura

Janar Babangida na wannan jawabi lokacin zantawa da manema labarai a Minna kafin bikin cikar Najeriya shekara 62 da samun ‘yanci, kamar yadda Gidan Talbijin na Channels ya ruwaito.

Don ganin haka, Janar Babangida ya ce akwai bukatar kowa ya kara himma.

Advertisement

Ya yaba wa kokarin gwamnatoci daban-daban a Najeriya wajen ganin kasar ta ci gaba da zama dunkulalliya, ya kuma yi kira don samun karin nasarori.

Ya ce burinsa shi ne ya ga Najeriya ta zama kasa mai karfi da yalwar arziki da hadin kai ta yadda zaman lafiya zai zarce komai.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending