Connect with us

News

Gwamnatin Najeriya ta yi ƙarar kamfanin Facebook tana neman ya biya tarar N30bn

Published

on

Facebook

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Hukumar kula da tallace-tallace ta Najeriya ta ce ta shigar da ƙarar kamfanin Meta mamallakin Facebook da Instagram da WhatsApp da wakilinsa kamfanin AT3 Resources Limited a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Advertisement

An tsinci sulalla tun na shekara 1,400 da suka wuce a wata rijiya a Isra’ila

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, hukumar ta ce ci gaba da wallafa tallace-tallace ga masu bibiyar Facebook da Instagram a Najeriya ba tare da tabbatar da samun amincewa kafin fitar da su ba, haramun ne, kuma take dokar tallace-tallace ce ta Najeriyar.

Advertisement

Hukumar ta ce kamfanin Meta ya ci gaba da yaɗa irin wadannan tallace-tallace da suka jawo wa gwamnatin tarayya asarar kuɗaɗen shiga.

Hukumar tana neman kamfanin na Meta ya biya tarar naira biliyan 30 kan take dokokin tallace-tallace da ya yi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending