News
An tsinci sulalla tun na shekara 1,400 da suka wuce a wata rijiya a Isra’ila
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Masu haƙar kayan tarihi a Isra’ila sun ce an gano wasu sulalla tun na ƙarni na bakwai, wato shekara kusan 1,400 da suka wuve kenan a ɓoye a cikin wata rijiya.
An samu sulallan masu nauyin giram 170 ne a wata rijiya Hermon a yankin Banias da aka ɓoye a wajen a shekara ta 635, kamar yadda ƙwararru suka ƙiyasta.
Trump ya maka gidan talabijin na CNN kotu
Sun ce sulallan sun ƙara bayyana ƙarshen Daular Byzantine ta Gabas a yankin.
Daular Rumawa ɗin ita ce rabin Daular Rumawa a gabas, wacce ta yi zamani fiye da shekara 1,000.
“Muna ganin kamar mai su ne ya ɓoye su a yayin da ake cikin barazanar yaƙi, da fatan wata rana zai koma ya kwashe kayansa,” in ji Yoav Lerer, shugaban tonon kayan tarihin.
Baya ga sulallan zinaren, an kuma sake gano ɓaraguzan gini da bututun ruwa da zulallan tagulla da sauran su a yayin haƙar, kamar yadda hukumomin Isra’ila suka ce.
Dr Gabriela Bijovsky, wata ƙwararriya a sha’anin kudin a cibiyar kayan tarihi ta Isra’ila ta ce yawancin sulallan na Sarki Phocas ne (602-610), amma mafi yawa na magajinsa ne Heraclius.
Yankin Banias yana da muhimmanci a addinin Kirista, saboda nan ne aka ce Yesu ya gaya wa abokinsa Peter cewa, “a kan dutsen nan, zan gina cocina.”
BBC
