Business
Mai kudin duniya na kokarin daidaitawa don saye Tuwita
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An jingine hada-hadar hannayen jarin Tuwita bayan wani rahoto ya bayyana cewa Elon Musk zai ci gaba da shirinsa na sayen dandalin sada zumuntar.
Mista Musk na shirin sayen Tuwita ne a farashin farko da ya taya watanni kafin ya watsar da cinikin, a cewar wasu majiyoyin Amurka.
Italiya ta bukaci a mika mata tsohon dan wasan kwallon kafa Robinho don fuskantar Shari’a
Hannayen jarin tuwita sun tashi da kusan kashi 13% kafin a dakatar da hada-hada.
Nan gaba a wannan wata ne aka tsara Elon Musk zai fuskanci kamfanin tuwita a gaban kotu bayan ya yi kokarin zare hannu daga cinikin.
Sai dai rahotanni sun ce ya aika wa tuwita wasika a cikin wannan mako inda ya yi tayin cewa zai martaba sharuddan da aka cimma a cinikin farko.
Elon Musk, mai yawan amfani da shafin Tuwita ne da mabiya sama da miliyan 100, ya yi tayin sayen duk hannun jari 1 a kan $54.20 (N39.500). Cinikin da aka kiyasta shi a kan kwatankwacin $44bn.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
