Connect with us

News

Mutum uku sun mutu a fashewar bam kan gadar da ta haɗe Rasha da Crimea

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Wata fashewa mai girman gaske a kan gada mafi tsawo a Turai ta kashe mutum uku a yankin Crimea da Rasha ta ƙwace daga Ukraine a 2014.

A cewar masu bincike, mutanen na cikin wata mota ne da ke kusa a lokacin da wata a-kori-kura ta tarwatse a kan gadar, abin da ya rusa wani ɓangare na gadar da ke da titi da kuma layin dogo na jirgin ƙasa.

Farashin Abinci Ya Ragu A Duniya In Ji Majalisar Dinkin Duniya

Rasha ta ce za a sake buɗe sashen layin dogon – inda tankokin man fetur suka kama da wuta – a yammacin yau Asabar.

Gadar wadda ke haɗe Rasha da yankin na Crimea, an buɗe ta ne a 2018 kuma alama ce ta ƙwacen da Rasha ta yi ba bisa ƙa’ida ba.

Advertisement

“Duk wani abin da aka yi ba bisa ƙa’ida ba, ya kamata a rusa shi, duk abin da aka sace sai an dawo wa da Ukraine kayanta, duk inda Rasha ta mamaye sai an ƙwato shi,” a cewar Mykhailo Podolyak, wani mai ba wa shugaban Ukraine shawara.

Sai dai bai amsa ko Ukraine ɗin ce ta kai harin ba.

BBC

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending