News
Wani ɗan majalisar dokokin Katsina ya rasu a Saudiyya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wani ɗan majalisar dokokin jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya, Dr Ibrahim Aminu Kurami, ya rasu a Saudiyya.
Ɗan majalisar mai wakilar mazaɓar ƙaramar hukumar Bakori ya je Saudiyyan ne don gabatar da aikin Umara, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Hadarin Mota Ya Yi Ajalin Mutum 3 A Neja
Wata majiya daga iyalansa ta shaida wa jaridar cewa ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya a Madina.
Marigayin ya rasu ya bara mata biyu da ƴaƴa 11 da kuma jikoki uku.
Advertisements
