Connect with us

News

Ginin coci ya danne mutane da dama a Anambra

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

 

 

 

Advertisement

Ana fargabar mutane da dama sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin wani coci da ya rushe a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.

 

Lamarin ya faru ne a jiya Lahadi a Cocin Katolika na Madonna Catholic a Iyiowa, da ke yankin Odekpe a ƙaramar hukumar Ogbaru, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Wani ɗan majalisar dokokin Katsina ya rasu a Saudiyya

Yankin na daga cikin yankunan jihar da dama da ke fama da ambaliyar ruwa da ake zaton ita ta jawo rushewar ginin.

 

Advertisement

Har yanzu ba a san adadin yawan wadanda lamarin ya rutsa da su ba yayin da ake ci gaba da aikin ceto a wajen.

 

 

 

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending