An rantsar da shugaban mulkin sojan Chadi, Mahamat Idriss Deby kan madafan ikon kasar kasar na tsawon wasu shekaru biyu bayan wata tattaunawa ta kasa da ‘yan adawa da manyan kungiyoyi masu dauke da makamai suka kaurace.
Manufar tattaunawar dai ita ce kawo karshen rikicin siyasar kasar.
Ginin coci ya danne mutane da dama a Anambra
A wajen tattaunawar an amince Mr Deby ya tsaya takara a zaben kasar da zai dawo da kasar Chadi kan mulkin farar hula.
Mahamar Deby ta dare kan karagar mulki a bara bayan kashe mahaifinsa Idriss Deby a wani farmaki da ya jagoranta kan ‘yan tawaye.
Amurka ta yi gargadin cewa za ta kakaba wa shugabannin sojojin Chadi takunkumi idan har suka tsawaita wa’adin miƙa mulki.
