News
Kungiyar ASUU ta janye yajin aiki
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar malaman jami’a a Najeriya, ASUU ta sanar da janye yajin aikin da mambobinta suka shafe wata takwas suna yi.
Dokta Chris Piwuna, mataimakin shugaban kungiyar ta ASUU ya tabbatar wa BBC labarin, inda ya ce an janye yajin aikin ne da sanyin safiyar Juma’a, bayan da shugabannin kungiyar suka gana jiya da daddare a Abuja babban birnin kasar.
Kazalika a sanarwar da shugaban ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke ya sanya wa hannu, ya ce sun janye yajin aikin ne duk da yake “ba a warware batutuwan da ake jayayya a kansu ba.”
Tun da farko, kotun daukaka kara a Najeriya ta umarci kungiyar ta janye yajin aikin gabanin ta saurari daukaka karar da ta yi a gabanta.
Tun ranar 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar malaman jami’o’in gwamnatin tarayyar Najeriya suka tsunduma cikin yajin aiki, suna neman gwamnatin ta biya musu wasu bukatu.
BBC HAUSA
