News
Wani Hadarin Mota Ya Yi Sanadin Rayuka 5, Ya Raunata 3 A Kogi – FRSC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Akalla mutane biyar ne suka mutu sannan wasu uku suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku a Kogi ranar Lahadi, kamar yadda Mista Stephen Dawulung, Kwamandan hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa (FRSC) na jihar Kogi ya bayyana.
Dawulung, wanda ya bayyana lamarin a matsayin “abin takaici matuka,” ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) a Lokoja a ranar Lahadin nan cewa hadarin mota ya faru ne a mahadar Ogbagbo da ke kan hanyar Ejule zuwa Ochadamu da misalin karfe 12.47 na rana. lokacin da wata mota kirar Nissan ta yi karo da wata motar Mazda.
Jaridar indaranka ta rawaito cewa, Kwamandan sashin ya bayyana cewa motar kirar Nissan ta kwace ta bar kan hannun da take tafiya a yinkurin kaicewa qani rami, zuwa wani hannun inda ta yi karo da motar Mazda 323 da ke zuwa.
Ambaliyar Ruwa: Gwamnati Ta Fara Kai Agajin Tan 12,000 Na Abinci Jigawa Da Anambra
“Abin takaici daga cikin mutane takwas da hatsarin ya rutsa da su, hudu sun mutu nan take yayin da hudu suka samu munanan raunuka.
“Jami’an mu da suka garzaya wurin da lamarin ya faru bayan an kai musu daukin gaggawa, sun ceto mutanen hudu da suka samu raunuka sannan aka garzaya da su asibitin Enemona da ke Ejule a karamar hukumar Ofu a jihar Kogi, inda mutum na biyar ya mutu a lokacin da yake jinya.
“An ajiye gawarwakin fasinjoji biyar da suka mutu a ma’ajiyar gawawwaki ta asibitin Enemona, a Ejule.
“Jami’an mu sun kawar da cikas da suka biyo bayan hadarin nan da nan daga hanyar don ba da damar zirga-zirgar ababen hawa,” in ji shi.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa, Kwamandan na FRSC ya ce abin da ya haddasa hatsarin ya hada da gudu da kuma rashin kyawun hanya.
Ya shawarci masu ababen hawa da su kula da bin ka’idojin da aka gindaya da kuma amfani da ka’idoji ta hanyar rage gudu a wuraren da aka gina da kuma sassan hanya masu muni.
Da yake jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, Dawulung ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba hanyoyin da za a bi wajen gyara manyan titunan da ya ce galibinsu na cike da ramuka. (NAN)
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News4 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
-
News22 hours ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
