News
Wata ƴar majalisa na son a kafa tsauraran dokoki kan luwadi da madigo a Nijar
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wata ‘yar majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar, ta yi kira ga ‘yan uwanta ‘yan majalisa maza da mata da su kafa wata dokar da za ta warware sarkakiyar da ke kunshe cikin dokokin kasar game da matsayin ‘yan luwadi da madigo.
Ambaliyar Ruwa: Gwamnati Ta Fara Kai Agajin Tan 12,000 Na Abinci Jigawa Da Anambra
Wannan na zuwa ne bayan da a makon jiya aka gurfanar da wasu mata da ake zargi da aikata madigo a gaban kotu, inda mai shari’ar ya kasa samun wata madogara daga dokokin kasar da zai iya amfani da ita wajen yanke musu hukunci.
‘Yar majalisar, Honorable Nana Djoubie Harouna Mati, ta shaida wa BBC cewa ‘yan kasar ne suka fito suka nemi majalisar da ta kafa doka da za ta haramta ayyukan ‘yan luwadi da madigo.
‘Yar majalisar ta ce bukatar hakan ya taso ne saboda a baya-bayan nan ne wani bidiyo ya nuna wasu ‘yan mata na yin madigo tsakaninsu wanda kuma ya zama tilas hukumomi su dauki mataki nan take.
Honorabul Nana Djoubie ta kuma ce babu wata doka a kasar ta hukunta mutum idan aka same shi da laifin yin madigo ko luwadi, adon haka haka ne suka tashi haikan wajen ganin sun kafa doka da ta kamata domin takawa lamarin burki tun bai ta’azzara ba.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
